Genesis 27:33 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ishaku ya yi makyarkyata ƙwarai ya ce, “To, wane ne wannan da ya farauto nama ya kawo mini kafin ka zo, har na ci na kuma sa masa albarka? Tabbatacce zai zama mai albarka!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ضَوَرْ جِكِے تَطٜىٰبِے إِسْحَٰڧَ سُواْسَيْ، يَثٜىٰ «تُواْ، وَنٜىٰنٜىٰ وَنَّنْ دَ يَڢَرَوْتُواْ نَامَ يَكَٰوُاْ مِنِ كَاڢِنْ كَذُواْ، حَرْ نَثِنْيٜىٰ نَسَ مَسَ أَلْبَرْكَ؟ عِ، بَابُ شَكَّ ذَيْ ذَمَ مَيْ أَلْبَرْكَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ishaku kuwa ya yi makyarkyata ƙwarai, ya ce, “Wane ne wannan fa, da ya farauto naman ya kawo mini, na kuwa cinye kafin ka zo, har na sa masa albarka? – i, albarkatacce zai zama.”