Genesis 27:36 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yaƙub ba? Ya yi mini ƙwace sau biyu ke nan; ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi yanzu kuma ya karɓi albarkata.” Sa’an nan ya yi tambaya, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِسُوَ يَثٜىٰ «أَيْ دَيْدَيْنٜىٰ عَكٜىٰثٜىٰدَشِ يَعْڧُوبَ؞ غَمَا يَيِ مِنِ ڨُوثٜىٰ حَرْ سَوْ بِيُ؞ يَا ڨُوثٜىٰ مَڟَيِنَ نَذَمَنْ طَنْ ڢَارِ، غَاشِ كُمَ يَنْذُ يَاڨُوثٜىٰ أَلْبَرْكَتَ؞» سَعَنً يَثٜىٰ وَبَابَنْ «بَابُ سَوْرَنْ أَلْبَرْكَرْ دَ كَضَغٜىٰ دُواْمِنَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yakubu ba? Gama sau biyu ke nan yake yi mini ƙwace. Ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi kuma, yanzu ya ƙwace mini albarkata.” Sa'an nan ya ce, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”