Genesis 27:38 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Ka albarkace ni ni ma, baba!” Sai Isuwa ya ɗaga murya ya yi kuka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِسُوَ يَثٜىٰ «بَابَنَ، أَلْبَرْكَ غُدَا كَطَيْ كَكٜىٰ دَ عِتَ؟ نِے مَا، كَسَا مِنِ أَلْبَرْكَ، يَا بَابَنَ!» سَيْ إِسُوَ يَطَغَ مُرْيَرْسَ يَيِ كُوكَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Har da ni ma ka sa mini albarka, babana.” Isuwa ya ta da murya ya yi kuka.