Genesis 28:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da ya kai wani wuri, sai ya dakata domin yă kwana, gama rana ta riga ta fāɗi. Ya ɗauki dutse daga cikin duwatsun wurin, ya sa shi ya zama matashin kansa, sa’an nan ya kwanta don yă yi barci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ يَكَيْ وَنِ وُرِے، سَيْ يَڟَيَ دُواْمِنْ دَرٜىٰ يَيِ دَيَكٜىٰ رَانَ تَا ڢَاطِ؞ يَطَوْكِ طَيَ دَغَ ثِكِنْ دُووَڟُنْ دَسُكٜىٰ أَوُرِنْ، يَطُواْرَ كَنْسَ عَكَيْ يَݣُونْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da ya isa wani wuri, sai ya kwana can a wannan dare, don rana ta riga ta faɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun da suke wurin, ya yi matashin kai da shi, ya kwanta, ya yi barci.