Genesis 29:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A can ya ga rijiya a jeji da garkuna uku na tumaki kwance kusa da ita, gama a wannan rijiya ce ake shayar da garkuna. Dutsen da ake rufe bakin rijiyar mai girma ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ يَدُوبَ، سَيْ يَهَنْغِ وَتَ رِجِيَ أَ ڢِيلِنْ ثِيَوَ دَ غَرْكٜىٰنْ تُمَكِ عُكُ عَݣُونْثٜىٰ كُسَدَ رِجِيَرْ، غَمَا دَغَ رِجِيَرْ نٜىٰ غَرْكُنَ سُكٜىٰ شَنْ ضُوَ؞ دُوڟٜىٰنْ دَ يَرُڢٜىٰ رِجِيَرْ كُوَ ڧَتُواْ نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da ya duba haka sai ya ga rijiya cikin saura, ga kuwa garken tumaki uku suna daura da ita, gama daga cikin rijiyar nan ake shayar da garkunan. Murfin rijiyar, dutse ne, babba.