Genesis 29:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سَاڢِيَ تَيِ يَعْڧُوبَ يَغَانٜىٰ، أَشٜىٰ لَيْعَتُ ثٜىٰ! سَيْ يَتَڢِے وُرِنْ لَبَنْ يَثٜىٰ مَسَ «مٜىٰ كٜىٰنَنْ كَيِمِنِ؟ بَ دُواْمِنْ رَحِيلَةُ ثٜىٰ نَيِ مَكَ عَيْكِبَ؟ تُواْ، دُوانْمٜىٰ كَرُوطٜىٰنِ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai'atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?”