Genesis 3:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ يَثٜىٰ «دَيَكٜىٰ يَنْذُ مُتُمْ يَا ذَمَ كَمَرْمُ، مَيْ سَنِنْ نَغَرْتَادَمُغُنْتَا؞ كَدَ يَمِيڧَ حَنُّنْسَ يَڟِنْكَ دَغَ ثِكِنْ یَیَنْ إِتَاثٜىٰ مَيْ بَادَ رَيْ، يَثِ يَرَايُ حَرْ أَبَدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.”