Genesis 30:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A lokacin girbin alkama, sai Ruben ya je jeji ya ɗebo manta-uwa ya kawo wa mahaifiyarsa Liyatu. Sai Rahila ta ce wa Liyatu, “Ina roƙonki ki ɗan sam mini manta-uwa ɗanki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَݣُونَكِنْ غِرْبِنْ أَلْكَمَ، سَيْ رَعُبَيْنُ يَتَڢِے يَسَامِ سَيْوَرْ طَوْكَرْ ثِكِ دَغَ دَاجِ، يَكَٰوُاْوَ مَامَرْسَ لَيْعَتُ أَغِدَا؞ سَيْ رَحِيلَةُ تَثٜىٰ وَ لَيْعَتُ «إِنَ ضُواْڧُوانْكِ كِطِبَ مِنِ دَغَ ثِكِنْ سَيْوَرْ طَوْكَرْ ثِكِ وَنْدَ طَنْكِ يَكَٰوُاْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kwanakin kakar alkama, Ra'ubainu ya fita ya samo manta uwa a saura, ya kawo wa mahaifiyarsa Lai'atu. Sai Rahila ta ce wa Lai'atu, “Ina roƙonki, ɗiba mini daga cikin manta uwar da ɗanki ya samo.”