Genesis 30:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma ta ce mata, “Bai ishe ki ba ne da kika ƙwace mijina? Yanzu kuma kina so ki ƙwace manta-uwa na yarona?” Sai Rahila ta ce “Shi ke nan, mijina zai iya kwana da ke yau saboda manta-uwa na ɗanki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لَيْعَتُ تَاثٜىٰ مَتَ «بَيْ إِشٜىٰكِبَ دَ كِكَ ڨُوثٜىٰ مِجِنَ؟ يَنْذُ كِنَ سُواْ كِڨُوثٜىٰ سَيْوَرْ طَوْكَرْ ثِكِ وَنْدَ طَانَ يَكَٰوُاْ؟» سَيْ رَحِيلَةُ تَثٜىٰ «تُواْ، مِجِنْمُ ذَيْ ݣُونَ دَكٜىٰ يَوْ عِدَنْ ذَاكِبَانِ سَيْوَرْ طَوْكَرْ ثِكِ وَنْدَ طَنْكِ يَكَٰوُاْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ta ce mata, “Kanƙanen abu ne da kika ƙwace mini mijina? Za ki kuma ƙwace manta uwar da ɗana ya samo kuma?” Rahila ta ce, “To, in haka ne, bari ya kwana tare da ke a daren yau a maimakon manta uwar da ɗanki ya samo.”