Genesis 30:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لُواْكَثِنْ دَ يَعْڧُوبَ يَدَاوُاْ دَغَ دَاجِ دَ يَمَّ، لَيْعَتُ تَاڢِتَ دُواْمِنْ تَسَدُ دَشِ؞ تَثٜىٰمَسَ «لَلَّيْ نٜىٰ ذَاكَ ݣُونَ دَنِے يَوْ، غَمَا كَاذَمَ سَكَمَكُواْ أَمَدَدِنْ سَيْوَرْ طَوْكَرْ ثِكِ وَطَنْدَ طَانَ يَكَٰوُاْ؞» سَيْ كُوَ يَݣُونَ دَ عِتَ أَدَرٜىٰنَّنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Yakubu ya komo daga saura da maraice, Lai'atu ta fita ta tarye shi, ta ce, “Sai ka shigo wurina, gama na riga na ijarar da kai da manta uwar da ɗana ya samo.” Saboda haka ya kwana tare da ita a daren nan.