Genesis 30:31 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Laban ya yi tambaya, “Me zan ba ka?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Kada ka ba ni wani abu. Amma in za ka yi mini abu guda ɗaya, zan ci gaba da kiwon garkunanka, ina kuma lura da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لَبَنْ يَثٜىٰ «تُواْ، مٜىٰنٜىٰنٜىٰ ذَنْبَاكَ؟» يَعْڧُوبَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «بَانَ بُڧَاتَرْ لَادَنْكَ؞ ذَنْ ثِيغَبَدَ لُورَ دَ غَرْكُنَنْكَ، عِدَنْ ذَاكَيَرْدَ دَ وَنَّنْ شَوَرَرْ دَ ذَنْبَاكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ce, “Me zan ba ka?” Yakubu ya ce, “Ba za ka ba ni kome ba, in da za ka yi mini wannan, sai in sāke kiwon garkenka in lura da shi,