Genesis 30:32 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bari in ratsa cikin dukan garkunanka yau in fid da masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki daga ciki, waɗannan ne za su zama ladana.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَتُواْ، يَوْ بَرِ إِنْبِے ثِكِنْ دُكَنْ غَرْكُنَنْكَ إِنْوَارٜىٰ دُكَنْ تُمَكِ دَ رَغُنَ مَاسُ كَلَرْ طِغُواْ طِغُواْ دَ كُواْوَنٜىٰ بَڧِنْ طَنْ ضَغُواْ دَ كُمَ أَوَكِ مَاسُ كَلَرْ طِغُواْ طِغُواْ؞ بَرِ إِرِنْ وَطَنَّنْ سُذَمَ لَادَنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
bar ni, in ratsa garkenka duka yau, in keɓe dukan masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki, waɗannan ne za su zama ladana.