Genesis 30:40 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yaƙub yă ware ƙananan garken dabam, amma sai yă sa sauran su fuskanci dabbobin da suke dabbare-dabbare da kuma baƙaƙe da suke na Laban. Ta haka ya ware garkuna dabam domin kansa bai kuwa haɗa su da dabbobin Laban ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَعْڧُوبَ يَوَارٜىٰ تُمَكِنْ دَغَ أَوَكِنْ؞ يَسَ تُمَكِنْ دَسُكٜىٰ مَاتَا سُكَ ڢُسْكَنْثِ تُمَكِنْ لَبَنْ مَاسُ ذَانِ ذَانِ دَ كُمَ بَڧَڧٜىٰ؞ تَهَكَنٜىٰ يَتَارَ وَكَنْسَ غَرْكٜىٰ يَكُمَ كٜىٰٻٜىٰسُ دَبَمْ دَ نَ لَبَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yakubu kuwa ya keɓe 'yan raguna, ya sa garkuna su fuskanci tsabgogin da ya shasshauta, da dukan baƙaƙen da suke cikin garken Laban. Sai ya ware waɗanda suke nasa, bai kuwa haɗa su da garken Laban ba.

Recommended Reading