Genesis 31:43 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Laban ya amsa wa Yaƙub, “Matan, ’ya’yana ne, ’ya’yansu, ’ya’yana ne, garkunan kuma garkunana ne. Dukan abin da kake gani, nawa ne. Duk da haka me zan yi a rana ta yau ga waɗannan ’ya’yana mata, ko kuma ga ’ya’yan da suka haifa?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً لَبَنْ يَأَمْسَ وَ يَعْڧُوبَ يَثٜىٰ «أَيْ، مَاتَنْكَ یَیَنَ نٜىٰ، یَیَنْسُ جِيكُواْكِنَ نٜىٰ، غَرْكُنَنْ دَبُّواْبِنَّنْ مَا غَرْكُنَنَ نٜىٰ؞ دُكْ أَبِنْدَ كَغَنِ أَنَنْ نَوَنٜىٰ؞ عَمَّا يَوْ أَݣَويْ وَنِ أَبِنْدَ ذَنْعِيَيِ غَمٜىٰدَ یَیَنَ مَاتَا، كُواْ كُوَ یَیَنْ دَ سُكَ حَيْڢَ نٜىٰ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, “'Ya'ya mata, 'ya'yana ne, 'ya'yansu kuma nawa ne, garkunan, garkunana ne, dukan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan yi a wannan rana ta yau ga waɗannan 'ya'ya mata nawa, ko kuma ga 'ya'yan da suka haifa?