Genesis 31:50 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Laban ya ce in ka wulaƙanta ’ya’yana mata, ko ka auri waɗansu mata ban da ’ya’yana mata, ko da yake babu wani da yake tare da mu, ka tuna cewa Allah shi ne shaida tsakaninka da ni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ كَوُلَڧَنْتَ یَیَنَ مَاتَا، كُواْ كُوَ كَعَوْرِ وَطَنْسُ مَاتَا عَكَنْسُ، كُواْدَيَكٜىٰ بَابُوَنِ تَرٜىٰدَمُو، تُنَ ڢَا، اللَّهْ شَيْدَ نٜىٰ ڟَكَانِينَ دَكَيْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan ka wulakanta 'ya'yana mata, ko kuma ka auri wata mata banda 'ya'yana mata, ko da yake babu kowa tare da mu, ka tuna, Allah shi ne mashaidi tsakanina da kai.”