Genesis 32:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da tsoro mai yawa da kuma damuwa, Yaƙub ya rarraba mutanen da suke tare da shi ƙungiyoyi biyu, haka ma garkunan tumaki da awaki, da garkunan shanu da raƙuma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَعْڧُوبَ كُوَ يَا جِڟُواْرُواْ سُواْسَيْ يَا كُمَ دَامُ، سَيْ يَرَرَّبَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ تَرٜىٰدَشِ دَ غَرْكُنَنْ تُمَكِ دَ أَوَكِ دَ نَشَانُو دَ نَرَاڧُمَ ڧُنْ‌غِيَ بِيُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yakubu fa ya tsorata ƙwarai, ya damu, sai ya karkasa mutanen da suke tare da shi, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu, da raƙuma cikin ƙungiya biyu,