Genesis 32:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya Ubangiji kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَعْڧُوبَ يَيِ أَدُّعَ يَثٜىٰ «يَا اللَّهْ نَكَكَنَ إِبْرَٰهِيمْ، اللَّهْ نَبَابَنَ إِسْحَٰڧَ، كَيْ يَهْوٜىٰهْ كَثٜىٰ مِنِ إِنْ كُواْمَ ڧَسَاتَ وُرِنْ یَنْعُوَنَ، ذَاكَ كُوَيِ مِنِ أَلْحٜىٰرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Yakubu ya ce, “Ya Allah na kakana Ibrahim, da mahaifina Ishaku, Ubangiji, wanda ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuwa yi maka alheri,’