Genesis 33:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yaƙub ya ce, “A’a, ina roƙonka, in na sami tagomashi a idanunka, sai ka karɓi wannan kyautai daga gare ni. Gama ganin fuskarka kamar ganin fuskar Allah ne, yanzu da ka karɓe ni da farin ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَعْڧُوبَ يَثٜىٰ «أَعَ، إِنَ ضُواْڧُواْ؞ عِدَنْ نَسَامِ ڢَضٍ جِنِ أَعِدُوانْكَ، كَكَرْٻِ ݣَوْتَادَغَ هَنُّونَ؞ غَمَا أَغَسْكِيَ غَنِنْ ڢُسْكَرْكَ كَمَرْ غَنِنْ ڢُسْكَرْ اللَّهْ نٜىٰ دَ إِرِنْ يَرْدَرْدَ كَكَرْٻٜىٰنِ دَ عِتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yakubu ya ce, “A'a, ina roƙonka, in dai na sami tagomashi a idonka, to, sai ka karɓi kyautar da yake hannuna, gama hakika ganin fuskarka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karɓe ni.