Genesis 33:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka bari ranka yă daɗe yă sha gaban bawansa, ni kuma in tafi a hankali bisa ga saurin abin da ake kora a gabana da kuma saurin ’ya’yan, sai na iso wurinka ranka yă daɗe, a Seyir.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
رَنْكَيَدَطٜىٰ، بَرِ كَوُثٜىٰ غَبَنَ، نِے كُوَ ذَنْبِے أَ حَنْكَلِ دَيْدَيْ بِسَغَ تَڢِيَرْ شَانُو دَ كُمَ بِسَغَ تَڢِيَرْ يَارَا، حَرْ سَيْ نَا إِسُواْ وُرِنْكَ عَيَنْكِنْ سٜىٰيِرْ أَ عٜىٰدُوامْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bari shugabana ya wuce gaban baransa, ni zan biyo a hankali bisa ga saurin shanun da yake gabana, da kuma bisa ga saurin yaran, har in isa wurin shugaba a Seyir.”