Genesis 33:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yaƙub kuwa, ya tafi Sukkot, inda ya gina wuri domin kansa, ya kuma yi bukkoki domin dabbobinsa. Shi ya sa aka kira wurin Sukkot.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا يَعْڧُوبَ يَتَڢِے سُكُّواتْ عِنْدَ يَغِنَ وَكَنْسَ غِدَا دَ بُكُّواْكِ دُواْمِنْ شَانُنْسَ؞ شِے يَسَا عَكٜىٰ كِرَنْ وُرِنْ سُكُّواتْ، وَتُواْ بُكُّواْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yakubu ya kama hanya zuwa Sukkot, ya kuwa gina wa kansa gida, ya yi wa shanunsa garke. Saboda haka aka sa wa wurin suna Sukkot.