Genesis 33:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ يَعْڧُوبَ يَ إِسُواْ بِرْنِنْ شٜىٰكٜىٰمْ وَنْدَ يَكٜىٰ أَ كَنْعَنَ، أَ حَنْيَرْسَ دَغَ ڢَدَّنْ أَرَمْ؞ يَا كُوَ كَڢَ ذَنْ‌غُوانْسَ كُسَدَ بِرْنِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yakubu kuwa ya kai birnin Shalem wanda yake ƙasar Kan'ana lafiya, a kan hanyarsa daga Fadan-aram, ya kuwa yi zango a ƙofar birnin.