Genesis 34:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka ce, “Waɗannan mutane ba su da damuwa, bari su zauna a cikin ƙasarmu, su kuma yi sana’a a ciki; ƙasar tana da isashen fili dominsu. Za mu iya auro ’ya’yansu mata, su kuma su auri namu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«وَطَنَّنْ مُتَنٜىٰ بَاسُ دَ دَامُوَ دَمُو؞ بَرِ سُيِ ذَمَ أَغَرِنْ سُيِ كَاسُوَنْثِنْسُ، غَمَا ڧَسَرْ تَنَدَ ڢَاطِ دُواْمِنْمُ دُكَ؞ بَرِ مُعَوْرِ یَیَنْسُ مَاتَا، سَعَنً مُو مَا مُبَاسُ یَیَنْمُ مَاتَا سُعَوْرَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Waɗannan mutane suna abuta da mu, ai, sai su zauna a ƙasar a sake, gama ga shi akwai isasshen fili a ƙasar dominsu. Bari mu auri 'ya'yansu mata, mu kuma mu aurar musu da 'ya'yanmu mata.