Genesis 36:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
یَیَ مَظَا نَدَنْغِنْ رٜىٰيُوٜىٰلْ طَنْ إِسُوَ سُونٜىٰ نَهَتْ دَ ظٜىٰرَ دَ شَمَّ دَ مِظَّ؞ وَطَنَّنْ نٜىٰ دَنْغُواْغِنْ رٜىٰيُوٜىٰلْ عَڧَسَرْ عٜىٰدُوامْ، ذُرِيَرْ بَسٜىٰمَتْ مَاتَرْ إِسُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, ɗan Isuwa. Shugaba Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza, waɗannan su ne shugabannin Reyuwel na cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.