Genesis 36:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً إِسُوَ يَطَوْكِ مَاتَنْسَ دَ یَیَنْسَ مَظَا دَ مَاتَا، تَرٜىٰدَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ غِدَنْسَ دَ كُمَ شَانُنْسَ دَ دُكَنْ كَايَنْسَ دَ يَسَامُ أَ كَنْعَنَ، سَيْ يَتَڢِے وَتَ ڧَسَا نٜىٰسَ دَ طَنْعُوَنْسَ يَعْڧُوبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Isuwa ya kwashi matansa, da 'ya'yansa mata da maza, da dukan jama'ar gidansa, da shanunsa, da dabbobinsa duka, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan'ana, ya kuwa tafi wata ƙasa nesa da ɗan'uwansa Yakubu.