Genesis 37:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا تَارِيحِنْ ذُرِيَرْ يَعْڧُوبَ؞ يُوسُڢَ، سَوْرَيِ نٜىٰ مَيْ شٜىٰكَرَا غُواْمَشَا بَݣَويْ؞ شِ دَ وَطَنْسُ یَنْعُوَنْسَ، وَتُواْ یَیَ مَظَا نَ بِلْهَ دَ نَ ظِلْڢَ، مَاتَانْ بَابَنْسَ، سُكَنْيِ كِيوُانْ غَرْكٜىٰنْ دَبُّواْبِے تَرٜىٰ؞ يُوسُڢَ يَكَنْ بَا بَابَنْسَ لَابَرِ غَمٜىٰدَ مُوغَيٜىٰنْ أَيُّكَنْ دَ یَنْعُوَنْسَ سُكَنْ عَيْكَتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu. Yusufu yana da shekara goma sha bakwai sa'ad da ya zama makiyayin garke tare da 'yan'uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin 'ya'ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da 'yan'uwansa suke yi a wurin mahaifinsa,