Genesis 37:36 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَ حَكَ، أَشٜىٰ، إِسْمَٰعِيلَاوَا دَغَ مَدْيَنَ سُنْرِغَا سُنْسَيَرْ دَ يُوسُڢَ غَ ڢُواْتِڢَرْ شُوغَبَنْ یَنْ غَادِنْ سَرْكِے ڢِرْعَوْنَ نَ مَصَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A lokacin kuwa, ashe, Madayanawa sun riga sun sayar da shi a Masar ga Fotifar, sarkin yaƙin Fir'auna, shugaba na masu tsaron fādar Fir'auna.