Genesis 37:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يُوسُڢَ يَسَاكٜىٰيِنْ وَنِ مَڢَرْكِ، يَكُمَ ڢَطَا وَیَنْعُوَنْسَ؞ يَثٜىٰ مُسُ «غَاشِ، نَسَاكٜىٰيِنْ وَنِ مَڢَرْكِ؞ نَغَ رَانَ دَ وَتَ دَ تَوْرَرِ غُواْمَشَا طَيَ سُنَ رُسُنَ مِنِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa 'yan'uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.”