Genesis 38:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yahuda ya ce wa surukarsa Tamar, “Ki yi zama kamar gwauruwa a gidan mahaifinki sai ɗana Shela ya yi girma.” Gama ya yi tunani, “Shi ma zai mutu, kamar ’yan’uwansa.” Saboda haka Tamar ta je ta zauna a gidan mahaifinta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَهُودَ يَثٜىٰ وَ تَمَرْ مَاتَرْ طَنْسَ «كِكُواْمَ غِدَنْ بَابَنْكِ كِيِ ذَمَنْكِ كَمَرْ مَثٜىٰنْ دَ مِجِنْتَ يَمُتُ، حَرْ طَانَ شٜىٰلَ يَيِ غِرْمَ؞» يَا ڢَطِ حَكَ غَمَا يَنَ جِنْ ڟُواْرُواْ كَدَ شٜىٰلَ كُمَ يَمُتُ كَمَرْ يَدَّ یَنْعُوَنْسَ سُكَيِ؞ تَهَكَ تَمَرْ تَا تَڢِے تَيِ ذَمَ أَغِدَنْ بَابَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar 'yan'uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta.