Genesis 38:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai ta tuɓe rigunan gwaurancinta ta rufe kanta da lulluɓi don ta ɓad da kamanninta, sa’an nan ta je ta zauna a ƙofar shigar Enayim, wadda take a hanyar zuwa Timna. Gama ta lura cewa ko da yake Shela yanzu ya yi girma, ba a ba da ita gare shi ta zama matarsa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ تَمَرْ تَتُوٻٜىٰ رِغَرْ جِكِنْتَ نَ مَاتَانْدَ مَذَنْسُ سُكَ مُتُ؞ تَايِ لُلُّٻِ دَ ڠَلٜىٰ، تَرُڢٜىٰ كَنْتَ، تَذَوْنَ عَبَاكِنْ ڧُواْڢَرْ عٜىٰنَيِمْ، وَدَّ تَكٜىٰ أَ حَنْيَ ذُوَا تِمْنَ؞ غَمَا تَا غَنِ ثٜىٰوَ شٜىٰلَ يَيِ غِرْمَ عَمَّا بَعَسَا تَا ذَمَ مَاتَرْسَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai ta tuɓe tufafinta na takaba, ta yi lulluɓi ta lulluɓe kanta, ta zauna a ƙofar Enayim a hanyar Timna, gama ta ga Shela ya yi girma, amma ba a ba da ita gare shi ba.