Genesis 39:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya sa a kurkuku, wurin da ake tsare ’yan kurkukun sarki. Amma yayinda Yusuf yake can a cikin kurkuku,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَيْغِدَنْ يُوسُڢَ يَطَوْكٜىٰشِ يَجٜىٰڢَ شِ عَكُرْكُكُ عِنْدَ عَكٜىٰ كُلّٜىٰ یَنْ كُرْكُكُنْ سَرْكِے؞ يُوسُڢَ يَذَوْنَ عَكُرْكُكُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Maigidan Yusufu ya ɗauke shi ya māka shi a kurkuku, inda 'yan sarƙa na sarki suke tsare, can ya zauna a kurkuku.