Genesis 4:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً كُمَ تَحَيْڢِ طَنْعُوَنْسَ، تَسَ مَسَ سُونَ هَبِيلَ؞ هَبِيلَ مَكِيَايِنْ دَبُّواْبِے نٜىٰ، كَيِنُ كُمَ مَيْ نُواْمَ نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne.