Genesis 4:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ظِلَّ، وَدَّ تَكٜىٰ مَاتَ تَبِيُنْ، تَحَيْڢِ تُبَلْ كَيِنُ، وَنْدَ يَذَمَ تُوشٜىٰنْ دُكَنْ مَاسُ ڧٜىٰرَ كَايَنْ تَغُلَّ دَ نَبَڧِنْ ڧَرْڢٜىٰ؞ یَرْعُوَرْ تُبَلْ كَيِنُ سُونَنْتَ نَعَمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zulai kuwa ta haifi Tubal-kayinu, shi ne asalin maƙeran dukan kayayyakin tagulla da na baƙin ƙarfe. Sunan 'yar'uwar Tubalkayinu Na'ama ne.