Genesis 4:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ءَادَمُ يَا سَاكٜىٰ ݣُونَ دَ مَاتَرْسَ، سَيْ تَحَيْڢِ طَا تَبَا شِ سُونَ شِيتُ؞ غَمَا تَاثٜىٰ « اللَّهْ يَسَاكٜىٰ بَانِ يَرُواْ أَمَدَدِنْ هَبِيلَ وَنْدَ كَيِنُ يَكَشٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai kuma Adamu ya san matarsa, ta kuwa haifi ɗa, ta raɗa masa suna Shitu, gama ta ce, “Allah ya arzuta ni da ɗa maimakon Habila wanda Kayinu ya kashe.”