Genesis 40:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ ݣُونَ عُكُ، ڢِرْعَوْنَ ذَيْثِرُواْكَ دَغَ كُرْكُكُ، يَمَيَرْ دَكَيْ أَمَڟَيِنْكَ، ذَاكَ كُمَسَا ݣُوڢْ نَ ڢِرْعَوْنَ أَ حَنُّنْسَ كَمَرْ يَدَّ دَا كَكٜىٰيِ مَسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
bayan kwana uku Fir'auna zai ɗaukaka ka, ya komar da kai matsayinka, za ka kuma sa finjalin Fir'auna a hannunsa kamar dā lokacin da kake mai hidimar shayarwarsa.