Genesis 40:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, a rana ta uku ne, ranar tunawa da haihuwar Fir’auna, ya kuwa yi biki wa dukan hafsoshinsa. Ya fid da shugaban masu shayarwa da kuma shugaban masu tuya a gaban hafsoshinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَ تَ عُكُ، وَدَّ عِتَثٜىٰ رَانَرْ تُنَاوَا دَ حَيْڢُوَرْ ڢِرْعَوْنَ، ڢِرْعَوْنَ يَيِ وَدُكَنْ دَتَّاوَنْسَ بِكِ؞ سَيْ يَثِرٜىٰ شُوغَبَنْ مَاسُ مِيڧَا وَسَرْكِے أَبِنْ شَا دَ شُوغَبَنْ مَاسُ غَسَ وَسَرْكِے غُرَاسَ دَغَ كُرْكُكُ، يَكَٰوُاْسُ غَبَنْ دَتَّاوَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir'auna, Fir'auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa.