Genesis 41:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
amma shekaru bakwai na yunwa za su biyo bayansu. Tsananin yunwar za tă sa a manta da dukan isashen abincin da aka samu a ƙasar Masar, yunwa kuwa za tă rufe dukan ƙasar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا بَايَنْسُ ذَاعَيِ شٜىٰكَرَا بَݣَويْ نَيُنْوَ؞ ڟَنَنِنْ يُنْوَ ذَاتَسَا أَمَنْتَادَ دُكَنْ عَبِنْثِنَّنْ دَ عَكَ سَامُ عَيَلْوَثٜىٰ نَڧَسَرْ مَصَرْ؞ يُنْوَ كُوَ ذَاتَ ثِنْيٜىٰ ڧَسَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar.