Genesis 41:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dalilin da aka ba wa Fir’auna mafarkan nan kashi biyu kuwa shi ne cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin. Allah zai aikata shi, ba da daɗewa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَيْمَيْتَاوَرْ مَڢَرْكِنَّنْ نَ ڢِرْعَوْنَ كُوَ، يَا نُونَ ثٜىٰوَ اللَّهْ يَا رِغَا يَا تَبَّتَرْ دَ ذَنْثٜىٰنْ، كُمَ اللَّهْ ذَيْسَا يَڢَرُ بَادَ جِمَاوَا بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Maimaitawar mafarkin nan na Fir'auna kuwa, ya nuna cewa Allah ya riga ya ƙaddara al'amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba.