Genesis 42:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya juya daga gare su ya yi kuka, sa’an nan ya dawo ya yi musu magana kuma. Ya sa aka ɗauke Simeyon daga gare su, aka daure shi a idanunsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يُوسُڢَ يَجُويَ وَنِ وُرِے، يَيِ كُوكَا؞ سَيْ يَسَاكٜىٰ كُواْمَاوَا وُرِنْسُ يَيِ مَغَنَ دَسُو؞ يَا طَوْكِ سِمٜىٰيُوانْ دَغَ ثِكِنْسُ يَسَا أَطَوْرٜىٰشِ أَعِدَنُونْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya juya waje ɗaya ya yi kuka, sai ya sāke komawa wurinsu ya yi magana da su. Ya ɗauki Saminu daga cikinsu ya ɗaure shi a kan idonsu.