Genesis 42:28 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya ce wa ’yan’uwansa, “An mayar mini da azurfata. Ga shi a cikin buhuna.” Zuciyarsu ta karai, suka dubi juna suna rawan jiki, suka ce, “Mene ne wannan da Allah ya yi mana?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْيَثٜىٰ وَیَنْعُوَنْسَ «غَاشِ، أَنْمَيَرْ مِنِ دَ كُطِنَ! يَنَنً عَبُهُنَ؞» سَيْغَابَنْسُ يَڢَاطِ، سُكَ جُويَا سُنَ كَلُّوانْ جُونَ سُنَ ضَوَرْ جِكِے سُنَثٜىٰوَ «مٜىٰ كٜىٰنَنْ اللَّهْ يَيِ مَنَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ce wa 'yan'uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!” Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?”