Genesis 42:33 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Sai mutumin wanda yake shugaba a kan ƙasar ya ce mana, ‘Ga yadda zan san ko ku mutane masu gaskiya ne. Ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku a nan tare da ni, ku ɗauki abinci domin gidajenku masu yunwa, ku tafi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُتُمِنْ، وَتُواْ ڠُومْنَنْ ڧَسَرْ، يَثٜىٰ مَنَ، ‹تُواْ، غَا يَدَّ ذَنْسَنِ كُواْ كُو مُتَنٜىٰ مَاسُ غَسْكِيَ نٜىٰ، كُبَرْ طَنْعُوَنْكُ طَيَ تَرٜىٰدَنِ، كُطَوْكِ حَڟِ دُواْمِنْ عِيَلَنْكُ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ثِكِنْ يُنْوَ، كُتَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sai mutumin, shugaban ƙasar, ya ce mana, ‘Ta haka zan sani ko ku amintattu ne, ku bar ɗan'uwanku ɗaya tare da ni, ku ɗauki hatsi domin iyalanku mayunwata, ku yi tafiyarku.