Genesis 42:35 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda suke juyewa hatsi daga buhunansu, sai ga ƙunshin azurfan kowane mutum a buhunsa! Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshe-ƙunshen kuɗi, suka firgita.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سُكٜىٰ جُويٜىٰ حَڟِنْ بُهُنَنْسُ، سَيْ كُواْوَ يَغَ كُطِنْسَ عَثِكِ؞ دَ سُو دَ بَابَنْسُ سُكَغَ ڧُنْشِنْ كُطَطٜىٰنْسُ، سَيْ سُكَجِڟُواْرُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da zazzagewar tayakansu ga ƙunshin kuɗin kowannensu a cikin taikinsa. Sa'ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshin kuɗinsu, suka razana.