Genesis 42:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, Yusuf ne gwamnar ƙasar wanda yake sayar da hatsi ga dukan mutanenta. Saboda haka sa’ad da ’yan’uwan Yusuf suka isa, sai suka rusuna masa har ƙasa da fuskokinsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يُوسُڢَ كُوَ شِينٜىٰ ڠُومْنَنْ ڧَسَرْ، شِينٜىٰ كُمَ مَيْسَيَرْ دَ حَڟِ غَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ؞ سَيْ یَنْعُوَنْ يُوسُڢَ سُكَذُواْ غَبَنْسَ سُكَ رُسُنَ دَ ڢُسْكُواْكِنْسُ حَرْ ڧَسَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu fa, Yusufu shi ne mai mulkin ƙasar, shi ne kuwa mai sayar wa jama'ar ƙasar duka. 'Yan'uwan Yusufu suka zo suka sunkuya har ƙasa a gabansa.