Genesis 43:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen dai suka firgita sa’ad da aka ɗauke su zuwa gidansa. Suka yi tunani, “An kawo mu nan ne saboda azurfan da aka sa a cikin buhunanmu da farko. Yana so yă fāɗa mana, yă kuma sha ƙarfinmu, yă ƙwace mu kamar bayi, yă kuma kwashe jakunanmu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ سُكَجِڟُواْرُواْ يَدَّ عَكَ كَٰوُاْسُ ثِكِنْ غِدَنْ يُوسُڢَ؞ سَيْ سُكَثٜىٰ «أَيْ، سَبُواْدَ كُطِنْ دَ عَكَ مَيَرْ مَنَ ثِكِنْ بُهُنَنْمُ أَ ذُوَانْمُ نَڢَرْكُواْ، شِے يَسَا عَكَ شِغَرْ دَمُو؞ يَنَسُواْ يَنٜىٰمٜىٰمُ دَ دَلِيلِ يَكَامَمُ، يَمَيْدَمُو بَايِ، يَكُمَ ڨُوثٜىٰ جَاكُنَنْمُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen suka tsorata sabili da an kawo su a cikin gidan Yusufu, sai suka ce, “Ai, saboda kuɗin da aka mayar mana cikin tayakanmu a zuwanmu na farko, shi ya sa aka shigar da mu, domin ya nemi hujja a kanmu, ya fāɗa mana, ya maishe mu bayi, ya kuma ƙwace jakunanmu.”