Genesis 43:28 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka amsa, “Bawanka mahaifinmu yana da rai har yanzu da kuma ƙoshin lafiya.” Suka kuma rusuna suka yi mubaya’a.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ أَمْسَ «بَاوَنْكَ، بَابَنْمُ يأَنَانً لَاڢِيَ؞» سَيْ سُكَ سُنْكُيَرْدَ كَوُنَنْسُ سُنَ رُسُنَ مَسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka amsa, “Bawanka, mahaifinmu yana lafiya, har yanzu yana da rai.” Suka sunkuya suka yi masa mubaya'a.