Genesis 43:33 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Aka zaunar da ’yan’uwan Yusuf a gabansa bisa ga shekarunsu, daga ɗan fari zuwa auta. ’Yan’uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ ذَوْنَرْ دَ یَنْعُوَنْ يُوسُڢَ أَغَبَنْ يُوسُڢَ بِسَغَ شٜىٰكَرُنْسُ نَحَيْڢُوَ دَغَ بَبَّ ذُوَا ڧَرَمِ؞ یَنْعُوَنْ كُوَ سُكَ دُدُّوبِے جُونَ سُنَ مَامَاكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Aka zaunar da 'yan'uwan Yusufu a gaban Yusufu bisa ga shekarunsu na haihuwa, daga babba zuwa ƙarami. 'Yan'uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki.