Genesis 43:34 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga teburin da yake a gaban Yusuf aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Benyamin ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ تٜىٰبُرِنْ دَيَكٜىٰ أَغَبَنْ يُوسُڢَ، عَكَ دِنْغَ طِبَنْ رَبُوانْسُ أَنَ كَيْ مُسُ، عَمَّا رَبُوانْ بِلِيَامِنُ يَا ڢِے نَكُواْوَنّٜىٰنْسُ سَوْ بِيَرْ؞ سَيْ سُكَثِ سُكَشَا تَرٜىٰدَ يُوسُڢَ سُكَجِ وَرَنْسُ دَاطِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga teburin da yake a gabansa aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Biliyaminu ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.