Genesis 44:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Muka kuwa amsa, ‘Muna da mahaifi tsoho, akwai kuma ɗa matashi, wanda aka haifa masa cikin tsufarsa. Ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kuwa ɗa kaɗai na mahaifiyarsa da ya rage, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُكَ أَمْسَ مَكَ، رَنْكَيَدَطٜىٰ، مُكَثٜىٰ، ‹مُنَدَ بَابَ ڟُواْهُواْ دَ طَنْ دَ عَكَ حَيْڢَ مَسَ أَڟُوڢَرْسَ، طَنْ أَوْتَنْمُ، وَنْدَ طَنْعُوَنْسَ يَا رِغَا يَا مُتُ؞ شِينٜىٰ كَطَيْ يَضَغٜىٰ ثِكِنْ یَیَنْ مَامَرْسَ، كُمَ بَابَنْسَ يَنَ ڧَوْنَرْسَ ڨُورَيْ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai muka amsa, ranka ya daɗe, muka ce, ‘Muna da mahaifi, tsoho, da ɗan tsufansa, auta, wanda ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai ya ragu daga cikin mahaifiyarsa, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’