Genesis 44:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mun ma dawo maka da kuɗin da muka samu a cikin bakunan buhunanmu daga ƙasar Kan’ana. Saboda haka me zai sa mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، كُطِنْ دَ مُكَ سَامُ عَبَاكِنْ بُهُنَنْمُ، بَمُنْ مَيَرْ مَكَ شِ دَغَ ڧَسَرْ كَنْعَنَ بَ؟ تَيَيَا ذَامُسَاثِ أَظُرْڢَا كُواْ ظِينَارِيَ دَغَ غِدَنْ مَيْغِدَنْكَ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga shi, kuɗin da muka samu a bakin tayakanmu, mun komo maka da su tun daga ƙasar Kan'ana, ta yaya fa, za mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka?