Genesis 45:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma sa’ad da suka faɗa masa kome da Yusuf ya faɗa musu, da kuma sa’ad da ya ga wagonun da Yusuf ya aika don a ɗauke shi a kai da shi can, sai ya farfaɗo, ya dawo cikin hankalinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا بَايَنْدَ سُكَ ڢَطَمَسَ دُكَنْ أَبِنْدَ يُوسُڢَ يَثٜىٰ مُسُ، سَعَدَّ كُمَ يَغَ كٜىٰكُنَنْ شَانُنْ دَ يُوسُڢَ يَعَيْكَ دُواْمِنْ سُكَيْشِ ڧَسَرْ مَصَرْ، سَيْ حَنْكَلِنْسَ يَدَاوُاْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma sa'ad da suka faɗa masa jawaban Yusufu duka, waɗanda ya faɗa musu, sa'ad da kuma ya ga kekunan shanun da Yusufu ya aiko don a ɗauke shi, sai ruhun mahaifinsu Yakubu ya farfaɗo.