Genesis 45:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنْيِ شٜىٰكَرَا بِيُ كٜىٰنَنْ دَ عَكٜىٰ يُنْوَ عَڧَسَرْ، عَمَّا يَا ضَغٜىٰ شٜىٰكَرَا بِيَرْ دَ بَذَاعَيِ نُواْمَ كُواْ غِرْبِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama shekara biyu ke nan da ake yunwa a ƙasar, amma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.